SALMAN KHAN; SHEKARU TALATIN DA BIYU A MASANA'ANTAR FIM (2)
SABON DECADE (2000-2005)
"Har Dil Jo pyar karega" da "Dulhan Hum Le Jayenge" sun shiga cikin Top 5 films of the year (2000). Film daya ya saki a 2001 'Chori chori chupke chupke'. A fina-finansa uku na 2002, 'Hum Tumhare Hain sanam' shi kadai yayi nasara, shi yasa baya cikin Top 3 actors a 2001 da 2002. Ya dawo cikin top 3 da nasarar "Baghban" da "Tere naam" a 2003. A 2004 "Garv" ya samu yabo sosai critically duk da baiyi tasiri ba commercially, shi yasa ma directorn film din Punit Issar ya fada a wata interview cewa "I think Garv was ahead of its times. For Salman, the movie had set a benchmark in terms of action sequences, drama and emotion. If it would have been released today then it would have definitely done business of Rs 200 crore,". "Mujhse Shaadi Karogi" yayi Hit Kuma ya shiga top 3 highest grossing films of 2004.
Salman Khan yayi kyakkyawan motsi a 2005, inda ya mamaye shekarar gabaki daya. "Maine Pyaar Kyun Kiya?" yayi HIT, "No Entry" ya zama Highest grosser of the year, take Salman ya buge Hrithik daga Number 2 spot.
FADI TASHI (2006-2009)
Hrithik ya samu gagarumar nasara da "Dhoom 2" da "Krrish" a 2006 inda ya dawo kan No.2 spot dinsa. Salman Khan yayi ta jero flops kafin ya samu super hit da "Partner (2007)". Kaf fina-finansa na 2008 babu Wanda yai nasara. Ya dawo da karfinsa a 2009 da film din "Wanted" wanda yayi babbar nasara har ya shiga top 3 highest grossing films of the year kuma ya bashi boosting da yake bukata a dai-dai wannan lokaci. Daga Nan, Salaman Khan era ta fara.
Mu hadu a Kashi na 3...
Habibu Maaruf Abdu
Comments
Post a Comment