SALMAN KHAN; SHEKARA TALATIN DA BIYU A MASANA'ANTAR FIM (3)

SALMAN KHAN ERA

Daga 2010 zuwa 2019 ba'a kiransa da decade idan ana maganar Bollywood sai dai ace "SALMAN KHAN ERA" saboda yadda ya mamaye kowanne lungu da sako kuma ya hana kowanne jarumi motsi. Masana sun tabbatar da cewa tun bayan wucewar "SUPER PHENOMENA" ta Rajesh Khanna, ba'a sake ganin wani complete dominance irin na salman khan a wannan lokaci ba. Ya abin ya kasance?


2010-2015:

Bayan fuskantar fadi-tashi daga (2000-2009), Salman Khan ya fara sabon decade da karamar nasarar 'Veer (2010)'. Bayan nan ne kuma, juyin juya hali mafi girma ya faru a tarihin Indian cinema saboda yadda Career salman khan ta kai kololuwar kurewa da nasarar "Dabanng 2010". A ranarsa ta farko, Dabanng ya goge duk wani tarihi inda ya zama Highest opener of all time. Ya wuce ya zama Highest opening week nett grosser a satin farko, bai tsaya ba sai da ya zama Second highest grossing film of all time a sati biyu kachal. Daga karshe yayi All time blockbuster Kuma Highest grosser of the year, Nan take Salman Khan ya yiwa Shahrukh Khan Juyin mulki ya hau No.1 spot.

Wannan nasara ta dabanng ta bawa kowa mamaki duba da irin kalubalen da Salman Khan ya fuskanta a baya. Ya za'a yi fim dinsa yayi irin wannan nasarar? Manyan jaridu irin su "Outlook, India today, Tehelka da kuma 'Brunch' har labarai suka buga a shafin bangonsu a kokarin fahimtar irin karbuwar da Salman khan yake da ita a wajen Yan kallo.

Yayinda wasu suke daukan nasarar dabanng kawai lucky yayi, Salman khan ya sake kafa wani tarihin na "Record non-holiday opener and grosser" da Blockbuster 'Ready' ya biyo bayansa da 'Bodyguard' – first Hindi film to gross Rs. 20 crore on a single day (record) duka a 2011, inda kuma suka zama top 2 highest grossers of the year. Salman khan ya zama jarumi na farko da yayi top 2 highest grossers of the year bayan da akai shekara 7 ba'a samu ba.

Yaci gaba da hana jarumai motsi a 2012. 'Ek Tha Tiger' ya kafa record na 'Highest-grossing domestic opening with ₹33.5 crore' Bayan nan, Shahrukh Khan ya saki 'jab Tak hai jaan' shi Kuma Aamir khan ya saki 'Talash' duk a shekarar ta 2012, Amma duka fina-finan babu wanda yazo kusa da Ek tha tiger ta bangaren nasara. Bayan da Salman khan ya saki 'dabanng 2' a shekarar, sai ya buge JTHJ da Talash kuma ya Zama 2nd highest grosser of the year. A lokacin box-office India suka tabbatar da cewa Salman Khan bashida abokin takara a kaf Bollywood inda sukace;

"The last few weeks have proved that Salman khan is a star just competing with himself as releases of other big stars have disappointed in terms of box-office collection. Jab Tak hai jaan and talash can be claimed to be big money makers but that is only because the main component (male star) of the budget has a share in profits and when the share is given, the profits are not great. The fact is that the, domestic theatrical box-office is not what it should have been.

Kamar yadda muka gani, duka wadannan fina-finan da Salman khan ya saki guda biyar sun zama manyan blockbusters, hakan yasa ya zama jarumin Bollywood na farko da ya taba yin blockbuster guda biyar kuma a jere cikin shekaru uku kachal. 

A lokacin, kawo 100crore bai zama gama gari ba, jarumai kokari suke ma su hada 75 crore, amma shi salman khan cikin sauki yake kawo ta kamar yadda box-office India suka fada "The 100 crore net mark which is redundant as a benchmark today has proved a stiff task for Shahrukh Khan, Ajay devgn and Aamir khan over the last few weeks while for salman starrers the question is not will it do 100 crore but in how many days!

A lokacin ne superstardom din salman khan ta Bayyana a zahiri. Masana sukai ta tattaunawa akanta inda suka tabbatar babu wani star da yake da stardom mai karfinta a wannan lokacin. Sun tabbatar stardom din itace hakikanin abinda yake bawa Fina finan Salman khan nasara kamar yadda Bollywood hungama suka fada cewa "It was sheer RAW stardom that enabled the film to take record starts as well as pose humongous lifetime totals"


Mu hadu a kashi na hudu

Habib Maaruf Abdu

Comments

  1. Lallai jarumi Salman Khan ya yi rawar gani a Bollywood. Amma na so a ce wannan rubutun kayishi da turanci don ba'a san iya inda zai tsaya ba sannan kuma Bollywood wood masana'anta ce wacce tai fice a duniya, kaga kuma turanci shine yaren da duk duniya ke ji... Allah kara basira abokina

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Kannywood movie review; Tsakaninmu

Kannywood movie review: Hauwa Kulu

NISAN KWANA FILM REVIEW; EXPLICATION